A cewar rahoton wakilin Kamfanin Dillancin Labaran Hauza a Najeriya, tattakin ya shiga rana ta biyu da ta uku a ranakun Juma’a da Asabar, 31 ga Yuli da 1 ga Agusta 2026. Mahalarta tattakin sun ci gaba da tafiya bayan sun gudanar da Sallar Asuba tare da cin karin kumallo, daga wuraren da suka yi zangon kwana.
A rana ta biyu, tattakin ya fara ne daga garin Karfi, inda mahalarta suka nufi hanyar da aka tsara. A kusa da garin Dakasoye, an gudanar da taron tunawa da shahidan harin bam na shekarar 2014, wanda ya rutsa da wasu daga cikin masu tattakin Arba’in na yankin Kano.
A yayin wannan taron tunawa, Shaikh Dakta Sunusi Abdulkadir ya gabatar da jawabi kan darussa da ake iya koya daga wannan lamari, sannan aka yi addu’a ga shahidan da suka rasa rayukansu sakamakon harin.
Daga nan ne mahalarta suka isa Yadakwari, inda suka tsaya domin gudanar da Sallah, hutawa da cin abinci, tare da sake tsara sahun masu tattaki domin ci gaba da tafiya cikin tsari.
Daga bisani tattakin ya ci gaba zuwa Chiromawa, inda aka yi zangon kwana na biyu. Bayan isar mahalarta, an gudanar da jawabin rufe ayyukan ranar tare da nasihohi da addu’o’in ƙarfafa gwiwa domin taimaka wa mahalarta su ci gaba da wannan ibada cikin haƙuri da juriya.
A rana ta uku kuwa, tattakin ya fara ne daga Chiromawa, wurin da aka yi zangon kwana na biyu. Bayan Sallar Asuba da karin kumallo, mahalarta suka ci gaba da tafiya da misalin ƙarfe 8:00 na safe.
A yayin tafiyar, mahalarta sun rera waƙoƙin juyayi da gudanar da makoki domin tunawa da zaluncin da aka yi wa Imam Hussaini (A.S.) da shahidan Karbala. Haka kuma sun bayyana ƙin amincewarsu da kisan da aka yi wa Imam Hussaini (A.S.), iyalansa da sahabbansa a Karbala.
A ci gaba da tafiyar, mahalarta sun tsaya a Kasuwar Dogo domin gudanar da Sallah da cin abinci, kafin daga bisani su ci gaba da tafiya zuwa wurin da aka tanada domin zangon kwana na uku.
Rahotanni sun tabbatar da cewa Tattakin Arba’in na yankin Kano na ci gaba da gudana cikin lumana, tsari da haɗin kai, tare da halartar dubban masu tattaki daga yankuna daban-daban, ciki har da Kano, Maiduguri, Azare, Nguru, Jigawa da sauran wurare.
Tattakin Arba’in na Imam Hussaini (A.S.) na gudana ne domin tunawa da cikar kwanaki arba’in da shahadar jikan Manzon Allah (S.A.W.A), tare da sabunta alƙawarin bin koyarwar Ashura da darussan sadaukarwa, haƙuri, jajircewa da tsayuwa kan gaskiya.
Haka kuma, wannan tattaki ya kasance wata hanya ta bayyana ƙauna da biyayya ga Ahlul Baiti (A.S.), tare da raya tunanin Imam Hussaini (A.S.) da kuma isar da saƙon Ashura ga al’umma.









Ra'ayinka